'Yan Nijeriya na mutuwa a Kogin Maliya

Yayinda ake ci gaba da kokawa game da matsalar masu fasakwaurin mutane daga wata kasa zuwa wata kasar, ofishin jakadancin Nijeriya a kasar Sudan ya koka game da hadarin da wasu 'yan kasar ke jefa kansu a ciki, a yunkurin zuwa Saudiya ta jirgin ruwa domin aikin hajji.

Ko a farkon wannan wata,mutane da dama ne, ciki har da 'yan Nijeriya, suka rasu, bayan da wasu kananan jiragen ruwa suka kife da su, bayan da suka tashi daga gabar Port Sudan a kan kogin Bahar Maliya a yunkurin zuwa Saudiyya.