Afurka Ta Kudu ta hau kujerar-na-ki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jacob Zuma, da Mu'ammar Gaddafi

Kasar Afurka Ta Kudu ta ki amincewa da yunkurin da Amurka ta yi na samun yardar mambobin Majalisar Dinkin Duniya don baiwa 'yan tawayen Libya kudin kasar da ke ajiye a Amurka

Amurkan dai ta ce tana so a yi amfani da kudaden ne wajen samar da tallafin gaggawa ga 'yan Libya, sai dai jakadan Afurka ta Kudu a Majalisar, Baso Sangqu, ya ce samar da kudaden zai nuna cewa Majalisar ta amince da gwamnatin 'yan tawayen ne, wanda kuma Majalisar, da Tarayyar Afrika ba su yi ba:

''Har yanzu ba mu yanke shawara ba ta amincewa da gwamnatin 'yan tawayen a matsayin halastacciyar gwamnati da ke wakiltar al'ummomin Libya, kuma kudirin ya nuna cewa tilas a mika kudaden ga wadannan 'yan tawaye.Wannan ne ya sanya muke kaffa-kaffa game da batun''.

Wasu fitattun 'yan kasar Afrika ta Kudun su dari biyu ne suka sanya hannu a wata takarda inda suka yi Alla-Wadai da matakin da kungiyar NATO ta dauka akan Libya.

'An yi wa Gaddafi tayin mafita'

A karon farko 'yan tawaye a Libya sun yi wa shugaba Gaddafi tayin mafita don ya fice daga kasar, idan har ya amince ya sauka daga karagar mulki.

Kazalika, 'yan tawayen sun yi tayin afuwa ga duk wani magoyin bayan Gaddafin idan har ya bayar da haske kan yadda za a kama shi- a raye ko a mace.