Tallafin Tarayyar Afrika ga Somalia

wasu masu fama da yunwa a Somalia
Image caption wasu masu fama da yunwa a Somalia

Shugabannin Afrika dake taro a birnin Addis Ababa sun yi alkawarin bada fiye da dala miliyan dari uku da hamsin domin taimakawa miliyoyin jamaar dake fama da matsalar fari da yunwa a yankin kusurwar gabacin Afrika.

Daga cikin wadannan kudade, dala miliyan dari uku za su fito ne daga Bankin raya kasashen Afrika.

Kungiyoyin kare Hakkin fararen hula sun nuna rashin jin dadinsu da yadda shugabannin hudu ne kawacal suka halarci taron.

Majalisar dinkin duniya dai ta ce dala biliyan dubu biyu da rabi ne ake bukata don taimakawa wadanda ke fama da yunwa a Somalia da kuma yankunan dake kewaye.

Makunni biyu da suka wuce ne dai ya kamata a yi taron , to amma aka dage shi domin baiwa wadanda suka shirya shi - wato kungiyar tarayyar Afrika -karin lokacin hada taron.