Yunkurin kame mahaifar Kanal Gaddafi

Yunkurin kame mahaifar Kanal Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen na fuskantar tirjiya daga dakarun Gaddafi

'Yan tawayen Libya na yunkurin kame garuruwan da suka rage a hannun Kanal Gaddafi ciki har da mahaifarsa ta birnin Sirte, bayan da suka kame birnin Tripoli.

Rahotanni sun bayyana cewa suna musayar wuta da dubban magoyan Gaddafi a kan hanyarsu ta zuwa garin na Sirte, wanda har yanzu yake hannun magoya bayansa.

Akwai kuma rahotannin sake barkewar fada a birnin Tripoli, bayan da birnin ya yi tsit da safe.

Shugaban 'yan tawayen Mahmoud Jibril ya nemi a kawo musu agajin gaggawa domin kaucewa jefa rayuwar mutane cikin hadari.

Ana fuskantar karancin abinci da ruwa da kuma wutar lantarki a Tripoli babban birnin kasar.

Har yanzu babu tabbas kan inda kanal Gaddafi ya ke, amma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce 'yan tawayen na yiwa wasu gine-gine kawanya inda suke tunanin Kanal Gaddafi na boye.

'Mun zaci za su mika wuya'

Ana saran Majalisar Dinkin Duniya za ta kada kuri'a a wannan makon domin duba yiwuwar sakin wasu kadarorin Libya da suka kai biliyan daya da rabi ga hukumar riko ta 'yan tawayen Libya.

Tun da Afrika ta Kudu ta yi kafar ungulu ga wani kokari na Amurka a Majalisar Dinkin Duniya na sakin na sakin kadarorin Libya da aka kwace.

Kasar Afrika ta Kudu ta kuma bukaci kotun manyan laifuka ta duniya da ta binciki kungiyar tsaro ta Nato game da yiwuwar keta hakkokin jama'a a Libya.

"Har yanzu mayakan Gaddafi na ci gaba da turjiya, mun yi mamaki," kamar yadda Fawzi Bukatif wani kwamandan 'yan tawaye ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Mun zaci za su mika wuya bayan da muka kwace birnin Tripoli daga hannunsu."

Karin bayani