Yaki da cin hanci ya yi rauni a Najeriya

Yaki da cin hanci ya yi rauni a Najeriya
Image caption Rahoton ya zargi EFCC da kasa yin katabus

Kungiyar Human Rights Watch mai kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa, ta ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na fuskantar zagon kasa daga bangarori da dama.

A wani rahoto da kungiyar ta fitar a kan hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, ta ce hukumar da Majalisun kasar da ma fadar gwamnati sun taimaka wajen dakile aikin yaki da dabi'ar ta cin hanci da kuma rashawa.

Kungiyar ta nuna rashin jin dadinta da hukumar ta EFFC, tana mai cewar duk da ana tuhumar mutanen da ake zargi da cin hanci da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa a Naijeriya, babu wani da aka daure bisa wani laifi.

Tana mai cewa aikin yaki da cin hanci da rashawa ya ja baya tun bayan da tsohon shugaban Hukumar ta EFCC Mallam Nuhu Ribadu ya bar aiki.

"Ni ban ga yadda za a yi a ce EFCC ta sha kakkausan suka da za a iya tabbatarwa ba bisa wannan rahoton," kamar yadda Femi Babafemi, mai magana da yawun EFCC ya shaida wa BBC.

'Batutuwa na zahiri da jitajita'

"An raba rahoton ne gida biyu, kashi daya an gina shi ne kan batutuwa na zahiri da gaskiya, yayin da aka gina daya bangaren kan jita-jita wadanda ba za ka iya amfani da su don cin nasara a wajen musu ba".

Yayin da aka tambaye shi cewa, akwai alamun da ke nuna yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na ja da baya, kuma ma wasu na ganin al'amarin ya mayar da gwamnati wani fage na aikata laifukan satar dukiyar jama'a? Sai ya ce:

"A'a, idan ka duba wannan batu da ake kira cin hanci da rashawa ko almundahana, ba batu ne da ya takaita ga Najeriya ba, ruwan dare ne gama duniya.

"Amma muhimmin batu shi ne, ko akwai yunkurin yaki da matsalar, tabbas zan gaya maka akwai, kuma wannan yunkuri na ci gaba," a cewar Femi Babafemi.