Za a yi taro game da batun yunwa

Taron Afurka game da yunwa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani yaro da ke fama da yunwa a Somalia

Shugabannin kasashen Afurka za su fara taro a Ethiopia a yau Alhamis da nufin samar da kudaden da za a tallafawa mutane miliyan goma sha biyu da bala'in yunwa ya shafa a wasu kasashen gabashin Afurka.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana bukatar dala biliyan biyu da rabi ne don taimakawa mutanen da bala'in yunwa ya shafa a Somalia da wasu kasashe da ke yankin.

Amurka, da Burtaniya, da China, da Japan, da Brazil, da Turkiya, da kuma kungiyar kasashen Musulmi, sun yi alkawarin ba da tallafi.

Sai dai akwai wasu 'yan Afurka da suka yi ta sukar gwamnatocinsu na gazawa wajen ba da tallafin a-zo-a-gani ga al'ummomin da bala'in yunwa ya shafa a kasashen kusurwar Afurka.