'yan tawayen Libya sun koma Turabulus

'Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan tawayen Libya

Yan tawayen Libya, sun mayar da gwamnatinsu babban birnin kasar Turabulus daga sansaninsu dake Benghazi, a kokarin su na tabbatar da iko a birnin.

Ministan mai da harkokin kudin 'yan tawayen, Ali Tahouni ne ya bada sanarwar, a taron manema labaru na farko da shugabannin 'yan tawayen suka gudanar a babban birnin kasar.

A waje daya kuma a wata sanarwar da aka watsa ta gidan talabijin din Benghazi, kakakin dakarun 'yan tawayen , Ahmed Bani ya nemi 'yan kasar da su tabbatar da tsaro a filayen jiragen sama, da guraren da ake ajiye manyan makamai da kuma kasar baki daya.

Kasar Italiya ta saki dalar Amurka miliyan 500 na Libya kuma za ta mika su ga 'yan tawayen.

Sai dai 'yan tawayen na fuskantar turjiya daga dakarun Gaddafi a yayinda suka dunfari Sirte mahaifar gaddafi.