Lauyoyi na takaddama da babban joji

Tutar Najeriya
Image caption Tutar Najeriya

A yau ne ake sa ran babban jojin Najeriya, Justice Aloysius Katsina-Alu zai rantsar da lauyoyi talatin da za'a baiwa matsayin SAN da ake baiwa manyan lauyoyi a kasar.

Sai dai kuma tuni wata takaddama ta kaure inda kungiyar lauyoyin Najeriyar wato NBA ta bukaci mambobinta hadi da wadanda za'a baiwa matsayin na SAN su kauracewa bikin.

Kungiyar na zargin cewa an sanya bikin a daidai lokacin taron da ta ke yi a Patakwal da nufin raba kan 'ya'yan kungiyar.

A baya-bayan nan dai bangaren shari'a na kasar na fuskantar kalubale dake barazana ga martabarsa.

Sai dai wasu lauyoyi cikin wadanda za'a baiwa matsayin SAN din sun lashi takobin halartar bikin.