Kungiyoyi sun amince a dauke barikoki

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou
Image caption Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin kare hakin dan adam da demokaradiyya sun goyi bayan shirin gwamnatin kasar na cire wasu barikokin soja daga cikin birnin yamai zuwa wasu yankuna na kasar.

Kungiyoyin na ganin kasancewar barikokin sojan a cikin garin Yamai abu ne da ke tattare da babban hadari.

Tun dai a lokacin mulkin rikon kwarya na sojoji da ya gabata ne, hukumomin na wancan lokacin suka bukaci fitar da wasu rundunonin soja daga yamai,matakin da sabuwar gwamnatin Issoufou Mahamadou ta goyi bayansa.