Afrika ta kudu ta yarda a ba Libya kudi

Dakarun 'yan tawaye a Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun 'yan tawaye a Libya

Kasar Afrika ta Kudu ta janye adawarta ga matakin Majalisar Dinkin Duniya na sakin dala biliyan guda da rabi na dukiyar Libya da aka kwace.

Za'a saki kudin ne domin gudanar da ayyukan jin kai, sai dai kasar ta bayyana damuwa na cewa kudaden ka iya shiga aljihun shugabannin yan tawaye.

Amurka ta so ta sa dole a kada kuri'a kan batun a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, amma daga bisani Afrika ta Kudu ta sassauto bayan Amurka ta amince ta janye lafazin gwamnatin 'yan tawaye daga yarjejeniyar.