Ban ki moon ya nemi a agazawa Libya

Sakataren majalisar dinkin duniya, Ban ki moon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakataren majalisar dinkin duniya, Ban ki moon

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su hada kai domin taimakawa Libya don ta fuskanci matsalar agajin da take bukata.

Ya ce karancin ruwan sha da abinci da man fetur da magunguna a Turabulus babban birnin kasar na yin barazana ga miliyoyin mutane.

Mr. Ban yace sun nemi kayan agaji na gaggawa da suka hada da magunguna da sauran abubuwan bukata na al'umma kamar ruwan sha da sauransu.