Mahaukaciyar guguwa na kadawa a Amurka

Mahaukaciyar guguwa Irene a Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mahaukaciyar guguwa Irene a Amurka

Mahaukaciyar guguwar da ake kira Irene mai matakin lamba daya ta isa Amurka inda ta janyo ambaliyar ruwa a arewacin jihar Carolina.

Tuni dai kimanin mutane dubu dari biyu da hamsin suka kasance ba su da wutan lantarki, yayinda igiyar ruwa mai karfi ta janyo ambaliyar ruwa.

An rufe hanyoyin zirga zirga tare da soke sauka da tashin jiragen sama a New York da wasu sauran manyan birane da guguwar zata ratsa.

Kimanin mutane dubu 300 ne aka umarta da su kauracewa yankunan da ake fargabar guguwar za ta ratsa.