A Pilato an dauki matakan sallah lafiya

Tutar Najeriya
Image caption Tutar Najeriya

Yayin da bikin karamar Salla ke karatowa, al'umomi da kuma hukumomin tsaro a jihar Filato na daukar matakan tabbatar da gudanar da shagulgulan Sallah lami lafiya.

Jihar ta Filato dai ta sha fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa, inda sau da yawa a lokutan manyan bukukuwa na addinai akan fuskanci hatsaniya.

To sai dai kuma a bana hukumomin tsaro da al'ummar musulmi da na kirista na fadakar da jama'a kan muhimmancin zaman lafiya don kaucewa hatsaniya a lokacin bikin sallar.