Ana zaman dar-dar a birnin Jos

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Filato na cewa ana ci gaba da zaman dardar a Jos babban birnin jihar bayan da aka samu wani sabon tashin hankali a ranar Litinin inda bayanai ke cewa an samu hasarar rayuka da kuma jikkata. Jihar ta Filato dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula na kabilanci da addini da kuma siyasa lamarin da ya sanya birnin Jos ya rarrabu.

Musulmai na da rinjaye a wasu unguwanni yayin da wasu unguwannin kuma kiristoci suka fi rinjaye. Tashin hankalin dai ya zo ne a daidai lokacin da wasu al'uma musulmi ke bikin karamar Salla a jihar bayan da suka kammala azumin Ramadan.

Rahotanni na cewa lamarin ya fi kamari ne a hanyar Rukuba, inda wasu matasa suka datse hanya inda suka hana wadanda suka halarci masallacin dake unguwar komawa gida bayan idar da Sallah.

Amma rudunar tsaro na kiyaye zaman lafiya a birnin ta ce ta shiga tsakani kuma tana yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya.