Julius Malema na Afirka ta Kudu zai fuskanci shari'a

Julius Malema na jam'iyyar ANC a Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tuhumar Julius Malema da yin kira da a kifar da gwamnatin kasar Bostwana mai makwabtaka da Afirka ta Kudu

Fitaccen dan siyasar nan na jam'iyyar ANC a kasar Afirka ta kudu, Julius Malema na fuskantar shari'a , wacce ka iya sa a kore shi daga jam'iyyar.

Ana zargin Mr. Malema da kuma wasu mutune biyar cikin jam'iyyar da yin kira da a kifar da gwamnatin Bostwana mai makwabtaka da Afirka ta kudun.

Mr Melama dai yana da goyan baya sosai daga matasa a cikin jam'iyyar ta ANC kuma makomarsa ka iya yin tasiri akan Shugaba Zuma wanda ke neman a sake zabarsa a matsayin shugaban jam'iyya a shekara mai zuwa