Kungiyar ECOWAS ta tallafawa Nijar

Nijar ta yi fama da karancin abinci
Image caption Nijar ta yi fama da karancin abinci

A jamhuriyar Nijar, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Africa ta yamma ECOWAS ko CEDEAO ta baiwa kasar wani tallafi na takin zamani don taimakawa wajen bunkasa ayyukan noma.

Ana sa ran cewa tallaffin takin da aka baiwa kasar jiya wanda ya kai dalar Amurka miliyan daya zai taimaka wajen samar da abinci wadatacce ga al'umomin kasar.

Nijar dai ta sha fama da matsaloli da suka jibanci karancin abinci wanda hakan ke haifar da yunwa a wasu lokuta.