Dakarun tsaro na murkushe 'yan adawa a Syria

Image caption Tankokin yakin Syria sun cika gari

Rahotanni daga Syria sun ce, dakarun tsaro sun killace wani gari da ke kusa da birnin Homs, a yankin tsakiyar kasar, a kokarin da suke na murkushe masu adawa da mulkin shugaba Bashar al-Assad.

A cewar masu fafutuka, an ji karar manyan bindigogi a kusa da kofar kudu, ta shiga garin Rastan, wanda hakan ya sa jama'a dayawa suka tsere daga gidajensu.

An kuma ce, sojoji da tankunan yaki sun afkawa garin Sarmeen, kuma rahotanni na cewa, an kara kai hare-hare akan wani kauye da ke kusa da iyaka da kasar Lebanon.

Shugaban kasar Turkiyya ya zafafa sukar da suke yiwa shugaba Assad.

ya ce, ya kamata ya daina kai hare-hare ba tare da bata lokaci ba, sannan ya biya bukatun jama'arsa.

Wakilin BBC ya ce, daga birnin Ankara na Turkiyya ne wasu 'yan adawan Syria suka bada sanarwar kafa majalisar wucin gadi mai mambobi casa'in da hudu.