'Yan tawaye sun baiwa dakarun Gaddafi wa'adin ajiye makamai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun 'yan tawayen Libya

Gwamnatin wucin-gadin Libiya ta ba dakaru masu biyaya ga Kanar Gaddafi, wa'adin nan da ranar Asabar, na su mika sauran manyan yankunan da ke karkashin ikonsu.

'Yan tawayen sun yi gargadin cewa, idan har dakarun suka ki yin biyaya, to fa za su afkawa mahaifar Kanar Gaddafin - watau birnin Sirte - da kuma wasu biranen biyu.

Shugaban Majalisar rikon-kwaryar Libiyan, Mustafa Abdel Jalil, ya ce ana tattaunawa da jami'an yankunan, domin ganin an mika su cikin ruwan sanyi.

Ya ce, fatanmu shine, dakarunmu su shiga Sirte, da yankunan tsakiyar Libiya, da kuma na kudancinta, ba tare da an sami wani tashin hankali na a zo a gani ba.

Sai dai a cewar wani wakilin BBC, fararen hula basu san abinda duniya ke ciki ba, saboda rashin wutar lantarki.