Birtaniya ta saki miliyoyin dalolin Libiya

William Hague, Sakataren harkokin wajen Birtaniya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption William Hague, Sakataren harkokin wajen Birtaniya

Gwamnatin Birtaniya ta ce, Majalisar Dinkin Duniya ta amince mata ta saki kimanin dala biliyan daya da rabi na Libiya, wadanda take rike da su a bankunan kasar.

A cewar sakataren harkokin wajen Birtaniyar, William Hague, wani babban cigaba ne aka samu, a kokarin da ake na agazawa jama'ar Libiya, kuma hakan zai taimaka wajen biyan bukatun gaggawa na mutanen kasar.

Kasashen Jamus da Faransa ma sun nemi izinin Majalisar Dinkin Duniya, na su saki biliyoyin daloli na kudaden Libiyan da aka hana tabawa.

Majalisar wucin-gadin Libiya ta ba dakaru masu biyaya ga Kanar Gaddafi, wa'adin nan da ranar Asabar, na su mika sauran manyan yankunan da ke karkashin ikonsu.