Stoke na neman aron Lukaku daga Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Romelu Lukaku

Kungiyar Stoke City na tattauna da Chelsea a wani yinkuri na neman aron sabon dan wasan da kungiyar ta siya wato Romelu Lukaku.

Chelsea ta sayo Lukaku ne mai shekarun haihuwa 18 a watan Agusta, kuma dan wasan ya taka leda a wasan da Chelsea ta doke Norwich da ci uku da guda.

Chelsea ta sayi Lukaku ne akan fam miliyan ashirin.

Dan wasan dai ya taka mahimmiyar rawa a kasar Belgiuwm bayan ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a kakar wasan shekarar 2009-2010.