Zanga zangar kyamar gwamnati a Syria

Image caption An gudanar da zanga zanga bayan sallar Idi

An gudanar da zanga zangar nuna kyamar gwamnati a dukan fadin kasar Syria, bayan da dubban jama'a suka kammala sallar Idi.

Rahotanni sun ce, dakarun tsaro sun hallaka akalla mutane bakwai.

A cewar wata kungiyar kare hakkin bil'adama, an kashe mutane ukku, sannan dayawa sun jikkata a garin Al-Harra, lokacin da sojoji suka bude wuta.

Masu fafutuka sun kuma ce, an bindige wasu mutanen ukku a lardin Daraa, sannan mutum guda ya mutu a birnin Homs.

A babban birnin Syrian kuma, watau Damascus, an ce masu zanga zanga da dama sun sami raunuka, a harbe-harben da aka yi a unguwannin da ke wajen birnin:

Wakilin BBC ya ce, duk da matsin da kasashen duniya ke cigaba da yiwa Syrian, ba alamun hukumomin kasar za su daina murkushe masu zanga zangar.