Shirin majalisar dinkin duniya akan kasar Libya

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dinkin duniya ta soma yunkurin shirya zabubbuka nan gaba a kasar Libya

Ana kara samun cikakkun bayanai game da yadda majalisar dinkin duniya a nan gaba, take shirin sanya kanta cikin harkokin kasar Libya.

Jami'in majalisar dinkin duniya na musamman a Libyan Ian Martin, yace yana tsammanin shugabannin majalisar rikon kwaryar kasar Libyan zasu nemi a taimaka masu, domin samar da wata rundunar 'yan sanda a kasar.

Shima Babban sakataren majalisar dinkin duniyar Ban Ki Moon ya bayyana cewa, mutanen kasar Libyan na bukatar taimakon kasashen duniya, ya kara da cewa nan da wasu 'yan kwanaki majalisar rikon kwaryar kasar Libyan zata turo masu da dukkanin bukatunsu.

Yace majalisar dinkin duniya ba zata bata lokaci ba ko kadan wajen biya masu wadannan bukatu

Bayanan da aka samu sun kuma nuna cewa majalisar dinkin duniyar na shirin kai wasu ma'aikatanta zuwa kasar Libyan, domin soma shirye shiryen gudanar da zabubbuka nan da wasu 'yan watanni masu zuwa

To sai dai majalisar wucin gadin kasar Libyan ta musanta cewa akwai sa hannun kasasahen duniya a cikin al'amuran kasar Libyan

Haka nan kuma majalisar dinkin duniya ta amince gwamnatin Burtaniya ta saki tsabar kudaden kasar Libyan da take rike dasu a cikin kasar.

Don haka gwamnatin Burtaniyan zata saki tsabar kudi har dala biliyan daya da rabi, kuma za'a yi amfani da wadannan kudade ne domin a tunkari ayyukan agaji da bunkasa tattalin arzikin kasar tare kuma da biyan ma'aikata albashin su