Tashin hankali a Jos

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filaton Nijeriya ke cewar wani sabon tashin hankali ya barke da ranar nan inda shedu suka ce sun ga gawawwakin mutane da kuma wadanda aka jikkata. Tashin hankalin dai ya faru ne a Unguwar Dutse Uku dake birnin na Jos. Jihar ta Filato dai ta sha fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa.

A bana daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu, kana a wannan makon mutane kimanin ashirin suka rasa rayukansu baya ga jikkata da kuma hasarar dukiya, a tashe-tashen hankula a Jos babban birnin jihar.