An kammala taron Paris kan Libya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Primiyan Biritaniya da Shugaban Faransa

Shugaban kasar Faransa, Nicholas sarkozy, ya ce dukkanin kasashen da suka halarci taron Paris domin duba makomar kasar Libya, sun dukufa wajen tabbatar da cewa an sakarwa kasar kadadrorinta da aka sanya wa takunkumi.

An dai sanya takunkumin ne akan kaddarorin kasar Liby da ke kasashen waje a lokacin mulkin shugaba gaddafi.

A lokacin da yake jawabi wajen wani taron manema labarai, Shugaba Sarkozy ya ce dukkan mahalarta taron sun goyi bayan shirin hadin kan kasar da za a gina kan ginshikin yafewa juna.

Tuni dai majalisar wucin gadin ta Libya ta fara kokarin tantance yawan kadarorin kasar ta Libya da ke kasashen waje.