Kasashen duniya na taro akan makomar Libya

'Yan adawa a Kasar Libya Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Kasashen duniya su sittin zasu yi taro domin duba makomar kasar Libya

Shugaba Sarkozy na kasar Faransa da kuma Fira Ministan Burtaniya David Cameron zasu jagoranci wani babban taro akan makomar kasar Libya yau a birnin Paris, yayinda gwamnatin rikon kwaryar kasar Libyar ke kokarin fadada ikonta.

Majalisar wucin gadin kasar Libyan zata bayyana irin abubuwan da kasar Libyan take bukata ba tare da wani bata lokaci ba ga tawaggar kasashen da zasu halarci taron su sittin, kana kuma ta bayyana abinda take son cimmawa a nan gaba.

Wannan kuwa ya hada da samar da tsaro da kuma dawo da kayan more rayuwa da kuma bayyana shirin da take yi dangane da siyasa da kuma farfado da tattalin arzikin kasar nan gaba.

Ana tsammanin kasasahen dake da burin yin huldar kasuwanci da Libyan zasu yi kokarin ganin cewar an kiyaye masu kadarorinsu a yayinda kamfanonin kasashen waje zasu shiga neman kwangilolin sake gina kasar