An samu baraka tsakanin masarauta da kuma gwamnatin Kano

Sallar Idi a Jahar Kano
Image caption An soma samin baraka tsakanin fadar masarautar Kano da kuma Gwamnatin jahar Kano a bana, dangane da hawan sallah karama

Gwamnatin jihar Kano tace tayi mamaki kan matsayin da fadar masarautar Kano ta dauka, na gudanar da hawan sallah duk kuwa da sanarwar da a da gwamnatin ta bayar tun da farko, na cewa ba za'a gudanar da kowane hawa ba saboda rashin lafiyar Sarkin na Kano.

Da yammacin jiya ne dai Sarkin da duka Hakimansa suka gudanar da Hawan Daushe, da a da gwamnatin tace shima ba za'a yi ba, bayan da rana ta bada sanarwar cewa za'ayi hawan.

Gwamnatin ta Kano dai tace ta bada sanarwar ne tun da farko sakamakon daidaito da suka samu da masarautar, cewa a soke yin duk wani hawa saboda rashin lafiyar Sarkin, Sai dai a nata bangaren masarautar tace hawa daya ne kawai aka shirya ba za'a gudanar ba, daga cikin guda hudun da ake yi kowace Sallah.

Wasu dai na ganin abinda ke faruwa, tamkar wata manuniya ce na irin rashin jituwar dake tsakanin masarautar ta Kano da kuma gwamnatin jihar, duk da cewa dai gwamnatin Kano'n na musanta hakan a kodayaushe.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya nemi jin ta bakin masarautar ta Kano dangane da wannan batu, sai dai an sanar masa cewa masarautar bata sami sanarwar matakin gwamnmatin ba a rubuce, don haka basu kaiga daukar wata matsaya ba.