Sama da mutum dari ne suka mutu a ambaliyar ruwan birnin Badun

Ta'alin ambaliyar ruwa a Najeriya
Image caption Sama da mutum dari ne suka hallaka a birnin Badun dake kudu maso yammacin Najeriya sakamakon wata ambaliyar ruwa data abkawa birnin a ranar juma'ar makon daya gabata

Kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya tace fiye da mutane dari ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan data abkawa kudu maso yammacin kasar.

Malam Umar Abdu Mai Riga, jami'i ne a kungiyar agajin ta Red Cross a Najeriya, ya kuma shaidawa BBC cewa mutame dubu daya da dari biyar ne suka rasa matsugunansu, wanda kuma ake tsugune dasu a wata makarantar boko a birnin na Badun. To sai dai yace yanzu yawan mutanen na raguwa a kullum

Yace wadanda suka rasa muhallan nasu na bukatar ruwan sha cikin gaggawa da kuma abinci, da kayayyaki irinsu shinfida sannan kuma da matsuguni mai kyau wanda ba dakin karatu ba

Jami'in yace akwai bukatar karin kayan agaji saboda yawan mutanen, duk kuwa da cewar hukumar kula da agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA da kuma gwamnatin jahar na yin iyakacin kokarinsu, a cewarsa

Ruwan saman daya sauka kamar da bakin kwaryar dai ya yi awon gaba da gidajen marasa galibu da dama a garin na Badun mafi girma na jahar ta Oyo.