Burtaniya da Amurka za su sasanta da Al -Qa'ida

Wani zane kan kungiyar Al-Qaeda Hakkin mallakar hoto n

Tsohuwar Shugabar hukumar leken asirin cikin gida ta Birtaniya, MI5 ta ce Amurka da Birtaniya na nazartar hanyoyin sasantawa tare da Al -Qa'ida domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya daga karshe.

Eliza Manningham-Buller ta ce akwai takaicin abinda martanin tsaro kan ta'addanci zai iya cimma wa, kuma dole ne a samu daidaiton siyasa a karshe.

Amma da take magana a wata laccar da BBC ta dauki nauyin shiryawa, Lady Manningham -Buller ta yi gargadin cewar har yanzu akwai sauran aiki ga yin sasantawar.

Madam Eliza Mannigham Buller ta jagoranci hukumar leken asirin har zuwa shekarar 2007.

Martani irin na soji ko na tsaro ga ta'addanci ba za su iya kaiwa gaci ba kamar yadda tsohuwar Shugabar hukumar leken asirin Birtaniya M15 ta ce, inda ta kara da cewa dole a dawo a nemi hanyoyin cimma maslahar siyasa.

Madam Eliza Manningham Buller wadda ta shugabanci hukumar ta MI5 tsawon shekaru biyar ta bayyana harin 11 ga watan Satumba a matsayin babban laifi amma ba yaki ba.

Ta dai bayyana cewa a nata ganin kalmar yaki da ta'addanci ba ta taimakawa, sannan kuma kutsen da aka yiwa Iraqi ya janye hankalin kasashen yammaci akan bin diddigin kungiyar Al Qaeda.

A lokacin da take gabatar da wata lakca a BBC mai taken ceto 'yanci, Madam Manningham Buller ta ce kutsen da aka yi wa Iraqi ya bayar da kofar Jihadi, sannan kuma ya baiwa wasu 'yan Birtaniya kwarin gwuiwar aikata ta'addanci.

Sai a ranar Talata mai zuwa ne dai za'a watsa lakcar da ta yi a sashen radio four na BBC.