Turkiya ta kori jakadan Israela

Jirgin ruwan Flotilla Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Daya daga cikin jiragen ruwan da Israela ta yi wa kutse

Kasar Turkiya ta kori jakadan Isra'ila sannan kuma ta jingine dukanin wasu yarjeniyoyin soji da take da su da ita bayan da Isra'ila ta ki neman gafara game da matakin sojin da ta dauka a kan wani jirgin ruwa dake kan hanyarsa ta zuwa Gaza a bara.

Ministan harkokin wajen Turkiya Ahmet Davutoglu, ya bayar da cikakken bayanin matakin kasar tasa, inda ya ce, Turkiya ba ta amince da takunkumin da Isra'ila ta saka a kan Gaza ba.

Kuma za ta tabbatar cewar kotun duniya ta binciki takunkumin da Isra'ila ta soma saka wa Gaza ranar 31 ga watan Mayu na 2010.

Matakin ya zo ne yan sa'o'i kafin wallafa wani rahoto da wani kwamitin binciken MDD ya yi game da farmakin na Isra'ila, wanda ya halaka masu fafutika 'yan Turkiya tara.

Wani kwafen da aka kwarmata ya ce toshiyar da Isra'ila take wa Gaza tana kan doka, amma kuma ya soki amfani da karfi.

Taka burki ga Diplomasiyya

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kasance mai tsami tun lokacin farmakin wanda Isra'ila ta bayyana a matsayin wani matakin kare kai.

Dama dai an taka burki akan duk wasu harkokin dangantaka tsakanin Turkiyya da Israila, bayan rikicin da ya biyo bayan mamayen da Israila ta yiwa wasu jiragen ruwa dake dauke da kayan agaji.

A yanzu kuma, an kara rage wannan huldar diplomasiyya ma baki daya, zuwa dan abun da ba za'a rasa ba.

Ministan harkokin wajen Turkiyya, Ahmet Davu-toglu, ya umarci Jakadan Israila, da ya kwashe ya na shi ya na shi ya fice daga cikin kasar nan zuwa tsakiyar makon gobe, sannan ya ce kowacce kasa za ta kuma janye sauran manya-manyan Jami'an diplomasiyyarta zuwa gida.

Ministan ya kuma ce za'a dakatar da duk wata yarjejeniya ta fuskar soji da ke tsakanin Turkiyya da Israila, yana mai alkawarin cewa gwamnatinsa za ta bayar da goyan baya ga duk wani yunkuri na gurfanar da Israila a gaban kuliya da mutanen dake cikin jirgin ruwa za su yi.

Jami'ai daga kasashen biyu, sun shafe wata da watanni suna kokarin sasantawa a tsakaninsu akan al'amarin da ya faru.

Sau uku ana jinkirta fito da rahoton na MDD domin bayar da damar yin haka, to amma a karshe Israila ta ki amincewa da bukatar da Turkiyya ta nema ta cewar akalla ma dai ta nemi afuwa akan al'amarin.