Bayanai kan hulda tsakanin Libya da CIA

taron kasashen duniya kan Libya
Image caption taron kasashen duniya kan Libya

Kungiyar kare Hakkin BilAdama ta Human Wright Watch ta ce ta gaano wasu takardun sirri a Libya, wadanda ke nuna cewa akwai dangantaka ta kut da kut tsakanin kungiyoyin leken asirin kasashen Yamma da gwamnatin Kanar Muammar al Gaddafi, bayan hare-haren 11 ga watan Satumba da aka kaiwa Amirka.

Peter Bouckaert , kakakin Kungiyar ta Human Rights Watch, ya ce, takardun sun nuna cewa kungiyar CIA ta tasa keyar mutane 8 zuwa 9 zuwa Libya, wadanda ake zargi da ta'addanci, kuma har ta turawa hukumomin Libyar irin tambayoyin da za a yi wa mutanen.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague, ya ce al'ammarin ya shafi gwamnatin Birtaniya ne da ta shude, kuma yanzu Birtaniya ta maida hankali ne a kan makomar Libya.