Za mu koma Turabulus, in ji 'yan tawaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mustafa Abdel Jalil

Shugaban majalisar wucin gadin Libya, Mustafa Abdel Jalil, ya ce 'yan tawayen za su dauke mazauninsu daga Benghazi zuwa Turabulus, babban birnin kasar, a makon gobe.

Ya kara da cewa a can ne 'yan tawayen za su ayyana kansu a matsayin sabuwar gwamnatin kasar Libya.

Da ya ke magana lokacin da ya koma kasar daga taron kasashen duniya da aka yi akan Libya, Mista Jalil ya ce an kafa wani kwamitin dattawa don sasantawa tsakanin dukkan bangarorin da ke kasar.

Ya ce an saki kashi talatin cikin dari na kaddarorin Libyar da aka rike a bankunan kasashen duniya saboda taimakawa al'ummomin kasar.