Shugaban kungiyar Larabarawa zai je Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ko Shugaba Bashar zai saurari Nabil Al Arabi?

Shugaban Kungiyar Kasashen Larabawa, Nabil al Arabi, ya ce yana da niyyar kai ziyara Syria a wannan makon don nuna damuwar kungiyar kan yadda aka shafe wata da watanni ana zubar da jini a kasar.

Zubar da jinin a sakamakon yinkurin murksushe masu zanga-zanga ne ta nuna adawa da gwamnati.

Mr al Arabi ya fadawa wani taron manema labarai cewa gwamnatin Syriar ta yi na'am da ziyarar tasa.

Ya ce, “Na yi imanin cewa duk lokacin da wani Babban Magatakarda na wata kungiya ya je wata kasa, to yana neman tabbaci daga hukumomin kasar.

“Saboda haka, zan tinkare su tsakani da Allah, in fada masu irin damuwar da muke da ita, kuma zan ji abin da za su fadi a kan haka.

A tashin hankali na baya-bayan nan, kafofin yada labarai, mallakin gwamnatin Syriar sun ce mutane shidda, galibinsu sojoji, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna kusa da birnin Hama.