Turkiyya za ta kai karar Isra'ila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ahmed Dovutoglu

Kasar Turkiyya ta ce tana shirin kalubalantar matakin killace Gaza da Isra'ila ta yi a gaban kotun duniya da ke birnin Hague.

Wannan dai ita ce alama ta baya-bayan nan ta yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu, tun bayan farmakin da Isra'ilar ta kai a kan wadansu jiragen ruwa da ke kai kayan agaji Gaza a bara, inda 'yan Turkiyya tara suka hallaka.

A jawabin da ya yi ta gidan talbijin na kasar, ministan harkokin wajen Turkiya, Ahmed Davutoglu, ya ce Turkiyya ba ta amince da sakamakon rahoton Majalisar Dinkin Duniya a kan farmakin ba, wanda ya ce killacewar da Isra'ilar ta yiwa Gaza bai sabawa doka ba.

Matakin dai ba zai yi wata barazana ba ga Israilar ba, domin zartar da hukunci game da batun ka iya daukar shekaru da dama.

Sai dai zai nuna cewa Turkiyya na da hanyoyin da za ta bi wajen dada dagula dangantakar da ke tsakaninta da Isra'ila.