Sabon tashin hankali a Filato

Image caption Jonah Jang

A Najeriya, a jiya da daddare ne wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a kauyukan Dabwak, da Farin Lamba da ke jihar Filato.

Kakakin gwamnatin jihar, Pam Ayuba, ya shaidawa BBC cewa an samu asarar rayukan mutane hudu, kuma kimanin mutane goma ne suka samu raunuka sakamakon harin.

Harin dai ya zo ne kimanin kwana guda bayan da aka kashe mutane takwas 'yan gida daya, da wadansu mutane uku matafiya a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar.

Jihar Filato dai ta sha fama da rikice-rikicen addini, da na kabilanci abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.