An ba dakarun kanar Gaddafi karin wa'adi

Mustafa Abdul Jalil
Image caption Mustafa Abdul Jalil

Shugaban majalisar wucin gadin kasar Libiya, Mustafa Abdul Jalil, ya ce za su ba dakaru masu biyaya ga Kanar Gaddafi, wadanda suka tare a wani gari da ke kudancin birnin Tripoli, wa'adin nan da karshen mako, na su mika kansu.

Daruruwan 'yan tawaye a cikin manyan motoci, dauke da manyan makamai, suna can sun sa garin Bani Walid a gaba, a cikin shirin ko ta kwana.

A wani bangare kuma, Birtaniya ta ce, za a gudanar da bincike mai zaman kansa, akan sabbin zarge-zargen cewa, jami'an leken asirin kasar sun yi hulda ta kut-da-kut da hukumomin tsaron Kanar Gaddafi.