An ba hamata iska a shariar Hosni Mubarak

Artabu tsakanin 'yan sanda da masu adawa da Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Artabu tsakanin 'yan sanda da masu adawa da Hosni Mubarak

A Masar an rika ba hamata iska, a ciki da wajen kotun da ake shari'ar tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak, a birnin Al-kahira.

Sai da Alkali ya dakatar da sauraron karar a lokuta da dama, yayin da fada ya barke tsakanin masu gabatar da kara, da kuma lauyoyin da ke kare tsohon shugaban, da kuma iyalan wadanda aka kashe a zanga-zangar.

Kotun ta saurari bahasin wasu shaidu inda wani babban jami'in dan sanda ya musanta cewa tsohon ministan cikin gidan kasar ya bada umranin a harbe masu zanga- zangar nuna kyama da gwamnatin Hosni Mubarak din.