Paul Biya zai sake yin takara a Kamaru

Image caption Taswirar Cameroon

Shugaban Kamaru, Paul Biya, na daga cikin sama da mutane arba'in da suka mikawa hukumar zaben kasar takardar tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar tara ga watan Oktoba.

Paul Biya, wanda ya shafe shekaru da dama a kujerar shugabancin kasar, zai sake tsayawa takarar ne karkashin jam'iyyar RDPC.

Zai fafata ne da wadansu tsofaffin 'yan takarar shugabancin kasar.

A baya dai, an yi ta cece-kuce dangane da dacewa ko rashin dacewar tsayawa takarar da Mista Biya zai yi.