Matsalar yunwa na yaduwa a Somalia

Kudancin Afrika Hakkin mallakar hoto NET
Image caption Kudancin Afrika na fama da matsalar fari da karancin abinci

Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsalar yunwar da ake fama da ita a kasar Somalia ta yadu zuwa wani karin yanki a Kudancin kasar.

Hakan dai na nufin kusan rabin Kudancin kasar na fama da matsalar yunwa. Wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya ta rabawa manema labarai ranar Litinin, ta ce hudu daga cikin yankuna takwas na Somalia na fama da wannan matsala.

Sanarwar ta ce kimanin mutane 750,000 na cikin hadarin rasa rayukansu cikin watanni hudu masu zuwa idan ba a dauki matakan da suka dace ba.

Ta kara da cewa a yanzu 'yan kasar ta Somalia miliyan 4 ne ke cikin hadari.

Mummunan fari a yankin Gabashin Afrika ya addabi kasar Soamalia a 'yan shekarun nan. Lmarin ya kuma shafi kasashen Kenya da Habasha da kuma Djibouti.