Za a yi zanga-zanga a Swaziland

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Mswati

A yau Litinin ne ake sa ran fara zanga-zanga ta mako guda a Swaziland don neman kafa dimokaradiyya da inganta rayuwa a kasar.

Gwamnatin Sarki Mswati, wanda shi ne sarki na karshe da ke shugabanci a nahiyar Afrika, na neman samun umurnin kotu don hana gudanar da zanga-zangar.

Gamayyar jam'iyun siyasa da kungiyoyin 'yan kasuwa da masu gangami ne dai suka shirya zanga-zangar.

Masu lura da al'amura sun ce wasu mutane na zargin sarkin ne da yin facaka da kudade, lamarin da ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.