Faduwar hannayen jari a Asia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasuwar hada-hadar hannayen jarin Asia

Farashin hannayen jari ya sake faduwa a kasuwannin hannayen jarin nahiyar Asia kamar yadda yake faduwa a kasuwannin hannayen jari ta kasashen Turai da Gabas mai nisa.

Kasuwannin hannayen jarin a kasashen Japan, da koriya ta Kudu da Hong Kong da kuma Australia sun fadi kasa warwas.

Hakan dai ya kara sanya mutane fargaba.

A yau Talata ne za a bude kasuwar hannayen jarin Amurka bayan da aka rufe ta saboda hutun da aka yi a kasar a jiya Litinin.