Musulmi sun zargi gwamnan Filato

Image caption Gwamnan Filato, Jonah Jang

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam da ke jihar Filaton Najeriya ta zargi gwamnatin jihar da nuna bambanci ga musulmi.

Kungiyar dai ta bayyana cewa gwamnatin na nuna bambanci wajen jajantawa da kuma kula da wadanda tashin hankali kan shafa a jihar.

Sakataren kungiyar, Malam Aminu Sadisu Abdullahi, ya ce: ''Daga kan shugaban jiha, da wadanda ke biye da shi, babu wanda ya je ya jajantawa al'uma( musulmi)''.

Sai dai kakakin gwamnatin jihar, Ayuba Pam, ya ce gwamnati bata nunawa kowa bambanci.

Jihar ta Filato dai ta sha fama da rikice-rikice masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.