Motocin soji sun shiga Nijar daga Libya

Yankin arewacin Nijar
Image caption Yankin arewacin Nijar

Wani ayarin motocin Libya kusan 50 dauke da muggan makamai, suna cikin Jumhuriyar Nijar bayan da suka tsallako daga Libyar.

Gidan talabijin na Al Arabiya ya ruwaito ministan harkokin wajen Nijar din, Bazoum Mohammed, yana cewa Kanar Gaddafi ba ya cikin ayarin motocin.

Wakilin BBC a Yamai ya ce daga bayanan da yake samu, ayarin motocin na kan hanyarsu ta zuwa Yamai, babban birnin kasar, kuma wasu sojojin Nijar na ba su kariya.

Shugabannin 'yan tawayen Libyar sun ce, sun yi imanin motocin na dauke da zinariya da tsabar kudi, abun dake nuna cewa wani ayarin motoci na nan tafe.

Tuni dai Burkina Faso mai makwabtaka da Nijar din ta yi tayin baiwa Kanar Gaddafi mafaka.

Kanal Gaddafi ya sha alwashin ci gaba da fada har zuwa karshe duk da cewa ya rasa iko da mafi yawan yankunan kasar.

Cikin kwarin gwiwa

Motocin sojin sun tsallaka zuwa Nijar ne inda suka isa birnin Agadez ranar Litinin da yamma, a cewar wata majiyar sojin Faransa da kuma Nijar.

Suka ce adadin motocin sun kai 200 zuwa 250 kuma sun samu rakiyar sojojin Nijar.

Wani mazaunin garin na Agadez ya shaida wa BBC cewa ya ga jerin gwanon motoci takwas suna wucewa, kuma an shaida masa cewa wasu karin motocin ma sun wuce.

Sai dai gwamnan jihar Agadez Kanal Mai Kido, ya shaida wa BBC cewa babu wasu jerin gwanon motoci da suka wuce.

Kasar Burkina Faso wacce ta hada iyaka da Nijar, ta yi tayin mafaka ga Kanal Gaddafi.

Matar Gaddafi, da 'ya'yansa maza biyu da mace daya sun tsallake zuwa kasar Algeria.

Mansur Daw ma ya shiga......

Akwai dadaddiyar hanya a yankin Sahara da ta hada Libya/Nijar zuwa garuruwan Airlit da Agadez.

Yawancin 'yan ciranin da ke kokarin shiga Turai daga Afrika ta Yamma kan yi amfani da hanyar, akwai kuma dubban jama'a da suke kaura daga Libya a 'yan watannin da suka wuce.

Ko a ranar Litinin ma, rahotanni sun nuna cewa shugaban tabbatar da tsaro a kasar ta Libya karkashin Kanar Gaddafi, ya isa birnin Yamai.

Rahotannin sun ce, Mansur Daw ya shiga Nijar din ne, tare da wasu tsoffin jami'an gwamnatin Gaddafi su kimanin goma, wadanda suka hada da Janar Ali Kanan da kuma Husseini al Kouni, tsohon jakadan Libya a Nijar din a farkon shekarun 2000.

Tawagar dai ta isa Nijar din ne tare da rakiyar tsohon shugaban kungiyar 'yan tawaye ta MNJ, Aghali Alambo.

Karin bayani