Obama ya yi kira ga 'yan Republican

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Obama ya na jawabi

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya yi kira ga 'yan jam'iyar adawa ta Republican da ke majalisar dokokin kasar da su taimaka wajen zartar da dokar da za ta samawa 'yan kasar sababbin ayyukan yi.

Shugaban ya yi kiran ne a yayin da yake yiwa ma'aikata jawabi a birnin Detroit, inda ake bikin ranar ma'aikata.

Ya ce ya kamata 'yan adawa su sanya kishin kasa a gaba wajen ci gaban tattalin arzikin kasar, ba wai baiwa siyasa fifiko ba.

Wadansu alkaluma da aka fitar ranar Juma'ar da ta gabata dai sun nuna cewa rashin aikin yi ya karu da fiye da kaso tara cikin dari, inda kuma a watan Agusta ba a samar da sabbin ayyukan yi a kasar ba.