Nijar ta baiwa mukarraban Gaddafi mafaka

Yankin arewacin Nijar
Image caption Yankin arewacin Nijar

Jamhuriyar Nijar ta baiwa wasu manyan mukarraban Kanal Gaddafi mafaka, ciki harda tsohon mai kula da harkokin tsaron cikin gida na Libyar Mansour Daw.

A ranar Litinin ne wani ayarin motocin sojin Libya kusan 50 dauke da muggan makamai, suka tsallaka kan iyakar kasar ta Sahara zuwa Jumhuriyar Nijar daga Libya.

Wakilin BBC a Yamai Iddy bara'u ya ce daga bayanan da yake samu, ayarin motocin na kan hanyarsu ta zuwa Yamai babban birnin kasar, kuma wasu sojojin Nijar na ba su kariya.

"Babu gaskiya a cikin rahotannin da ke cewa Kanal Gaddafi na cikin jerin gwanon motocin da suka shigo Nijar," a cewar ministan harkokin cikin gida na Nijar Mr Abdou Labou.

"Nijar a matsayinta na kasa mai maraba da jama'a za ta saurari duk wata bukata ta baiwa Kanal Gaddafi mafaka," kamar yadda Mr Labou ya shaida wa BBC.

Shugabannin 'yan tawayen Libyar sun ce, sun yi imanin motocin na dauke da zinariya da tsabar kudi, abun dake nuna cewa wani ayarin motoci na nan tafe.

Kanal Gaddafi ya sha alwashin ci gaba da fada har zuwa karshe duk da cewa ya rasa iko da mafi yawan yankunan kasar.

Amurka na da damuwa

Amurka ta ce bata tunanin cewa Kanal Gaddafi na cikin jerin motocin da suka shiga Nijar din.

"Bamu da masaniya kan inda Gaddafi ya ke a yanzu bayan Libya," a cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Victoria Nuland.

"Muna kira da babbar murya ga gwamnatin Nijar da ta kame wadanda suka shiga kasarta ta, wadanda ka iya sa kasancewa cikin masu laifi," a cewar Nuland.

Sai dai ta kara da cewa manyan jami'an gwamnatin Kanal Gaddafi na cikin jerin gwanon motocin da suka shiga kasar ta Nijar.

Cikin kwarin gwiwa

Motocin sojin sun tsallaka zuwa Nijar ne inda suka isa birnin Agadez ranar Litinin da yamma, a cewar wata majiyar sojin Faransa da kuma Nijar.

Suka ce adadin motocin sun kai 50 ko fiye da haka kuma sun samu rakiyar sojojin Nijar.

Wani mazaunin garin na Agadez ya shaida wa BBC cewa ya ga jerin gwanon motoci takwas suna wucewa, kuma an shaida masa cewa wasu karin motocin ma sun wuce.

Sai dai gwamnan jihar Agadez Kanal Mai Kido, ya shaida wa BBC cewa babu wasu jerin gwanon motoci da suka wuce.

Matar Gaddafi, da 'ya'yansa maza biyu da mace daya sun tsallake zuwa kasar Algeria.

Mansur Daw ma ya shiga......

Akwai dadaddiyar hanya a yankin Sahara da ta hada Libya/Nijar zuwa garuruwan Airlit da Agadez.

Yawancin 'yan ciranin da ke kokarin shiga Turai daga Afrika ta Yamma kan yi amfani da hanyar, akwai kuma dubban jama'a da suke kaura daga Libya a 'yan watannin da suka wuce.

Ko a ranar Litinin ma, rahotanni sun nuna cewa shugaban tabbatar da tsaro a kasar ta Libya karkashin Kanar Gaddafi, ya isa birnin Yamai.

Rahotannin sun ce, Mansur Daw ya shiga Nijar din ne, tare da wasu tsoffin jami'an gwamnatin Gaddafi su kimanin goma, wadanda suka hada da Janar Ali Kanan da kuma Husseini al Kouni, tsohon jakadan Libya a Nijar din a farkon shekarun 2000.

Tawagar dai ta isa Nijar din ne tare da rakiyar tsohon shugaban kungiyar 'yan tawaye ta MNJ, Aghali Alambo.

Karin bayani