Yobo ya koma Fenerbahce na wucin gadi

Image caption Joseph Yobo ya takawa Fernabahce leda a kakar wasan bara

Dan wasan Everton Joseph Yobo, ya sake komawa kungiyar Fenerbahce ta kasar Turkiyya na wucin gadi a kakar wasan bana.

Dan wasan Najeriyar mai shekarun haihuwa 31, ya taka leda ne a kakar wasan bana, inda ya taimakawa kungiyar lashe kofin Super Lig championship.

Kwantaragin Yobo, da Everton zai kare ne a shekarar 2014.

"Ina matukar murna an warware matsalolin dake tsakanin Everton da Fernabache." In ji Yobo.

"Ina farin ciki saboda na koma kungiyar da raina ya kwanta kuma na ji dadin takawa kungiyar leda a bara."

Fenerbahce dai sun nemi su sayi dan wasan na dindindin amma ta kasa cimma yarjejeniya da Everton.