Ana taro a birnin Algiers kan tsaro

Ministocin waje daga kasashen arewacin Afrika na wani taro a Algiers, babban birnin kasar Algeria, domin tattaunawa akan hanyoyin da za a bi kan yadda tunkari ta'addanci da hana bazuwar makamai a yankin daga Libya.

Akwai manya manyan wakilai daga kasashen Faransa da Amurka da suke halartar taron na kwanaki biyu.

Kasar Algeria ta nuna damuwa akan cewa makamai daga Libya ka iya fadawa hannun reshen Alqa'ida na yankin Magreb, wadanda suke gudanar da aikace aikacensu a yankin Sahara, inda suke kama mutane suna garkuwa da su.

Jami'an diplomasiyya daga Mali, da Niger, da Mauritania su ma suna halartar taron.