Yau za'a bude wani taro kan fari a Kenya

Image caption Matsalar fari a Somalia

Yau ne za'a bude wani taron hadin gwiwa na kwanaki biyu dan gano bakin zaren bala'in farin da ake yawan fuskanta a kasashen kusurwar gabashin Afurka.

Taron dai na hadin gwiwa ne tsakanin Majalisar dinkin duniya da bankin duniya da kuma mai daukar bakuncin taron wato gwamnatin kasar Kenya.

Prayim ministan Kenya, Raila Odinga ne zai jagoranci taron.

A duk lokacin da aka samu barkewar bala'in fari dai a kasashen kusurwar Afurka, wadanda lamarin ya shafa na tsallakawa ne zuwa kasar ta Kenya.

Ana sa ran cewa shugabannin da minitocin yankin zasu halarci taron.