A yau za'a ci gaba da shariar Hosni Mubarak

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga da 'yan sanda na taho mu gama da juna

A yau ne za a ci gaba sharia kan tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak a birnin Alqahira. An daga shariar da kwana guda, bayanda rikici ya kaure a kotun a ranar Litinin tsakanin magoyabayansa da masu adawa da shi.

A wajen kotun kuma, masu zanga zanga sun yi dauki ba dadi da yan sanda.

Wani me goyon bayan Mubarak ya rike hoton tsohon shugaban kasar Masar yayinda yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a lokacin boren suka cinama hotun wuta.

Masu shigar da kara sun kira wasu manyan jamian yansanda su hudu wadanda ake ganin zasu gabatar da shaida akan irin rawar da Mr Mubarak ya taka wurin murkushe masu zanga zanga.

Sai dai a cewar daya daga cikin lauyoyin, mutumin daya fara gabatar da shaida ya ce shi be san da umurni a harbi masu zanga zangar ba .