Ana kaiwa 'yan Afrika bakar fata hari a Libya

Wasu 'yan Afrika masu ci rani a Libya
Image caption Wasu 'yan Afrika masu ci rani a Libya

Kungiyoyin agaji sun ce daruruwan bakaken fata 'yan Afrika masu ci rani a Libya sai ta ficewa suke yi suna barin kasar a kowace rana saboda tsoron kai masu hare-hare da ke da alaka da nuna bambancin launin fata.

Ofishin Kungiyar dake kula da kaurar Jama'a ta duniya dake jumhuriyar Nijar, ya ce harin nuna kin jinin baki ya karu tun bayan da 'yan tawayen da ke gaba da Gaddafi suka kara mallakar wasu yankuna a kasar ta Libya.

Wadanda suka tsere sun ce ana kallon duk wani bako a Libya tamkar mai alaka da sojin hayar Kanar Gaddafi.