NATO ta ce sojinta ne ya kashe wani wakilin BBC a Afghanistan

Dakarun NATO a Afghanistan
Image caption Dakarun NATO a Afghanistan

Dakarun kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan, sun ce wakilin BBC da aka kashe a can a watan Yuli, wani sojan Amerika ne ya harbe shi.

Ahmed Omed Khpulwak, wanda ke aiko wa sashen harshen Pashto na nan BBC da rahotanni, ya rasu ne a lokacin wani harin kunar bakin wake a Lardin Uruzgan.

Rahotannin farko sun nuna cewa 'yan Taleban ne suka kashe shi, amma yanzu wani binciken kungiyar tsaro ta NATO ya tabbatar cewa wani sojan Amerika ne ya harbe, bayan da ya yi kuskuren zaton cewa shi dan harin kunar bakin wake ne.

Babban Darektan Labaran Duniya na BBC, Peter Horrocks, ya yi yabo ga Ahmad Omed Khpulwak. Ya ce yana da muhimmanci 'yan jarida su sami kariya mafi inganci domin duniya ta sami jin labaran da suke bayarwa.